Mahukuntan Iraki sun bayyana cewa: Ana ci gaba da samun tururruwan jama'a da suke zuwa birnin Karbala domin gudanar da juyayin ranar Ashura a ranar goma ga watan Muharram lamarin da ke nuni da cewa; Akwai yiyuwar yawan jama'ar da zasu halacci juyayin a bana zai haura mutane miliyan uku.
Jamal Shahristani shugaban bangaren sanarwa a cibiyar kula da masu ziyarar wajaje masu tsarki a kasar Iraki a jiya Asabar ya bayyana cewa: A halin yanzu haka birnin Karbala tana ci gaba da karbar baki daga ciki da wajen kasar da suka zo domin gudanar da juyayin ranar Ashura a ranar 10 ga watan Muharram, don haka ake hasashen yawan jama'ar da zasu halacci juyayin na bana zai haura mutane miliyan uku, inda ko a shekararda ta gabata fiye da mutane miliyan biyu ne suka gudanar da juyayin.
A yau Lahadi ne dai za a gudanar da zaman taron juyayin Ashura a birnin Karbala na kasar Iraki domin jaddada alhini da juyayi kan gisan gillar da Bani-Umayyah da magoya bayansu suka yi wa jikan manzon Allah kuma daya daga cikin shugabannin samarin gidan aljanna Imam Husani dan Ali dan Abi-Talib {a.s} da iyalan gidansa da sahabbansa da ba su wuce 72 ba, a filin Karbala na kasar Iraki a shekara ta 61 bayan hijira, bayan sun bijirewa mulkin kama karya da bakin zalunci na mahukuntan Bani-Umayyah karkashin ja'irin shugaba Yazid dan Mu'awiya da dukkanin Musulmi suka yi tarayya kan fasikancinsa da rashin cancantarsa ga jagorancin al'ummar musulmi. 288